Gwamna Masari Na Jihar Katsina Yasha Alwashin Kafa Kasuwar KilishiGwamnatin jihar Katsina karkashin shugabancin Gwamna Aminu Bello Masari ta sha alwashin gina katafariyar kasuwar kilishi ta zamani a garin Kayauki dake a karamar hukumar Batagarawa ta jihar.

Gwamnan jihar ya bayyana hakane lokacin da wata kungiyar ci gaban Karamar hukumar ta kai masa ziyara a ofishin sa dake gidan Muhammadu Buhari.

Gwamnan yace yanzu haka dai ma’aikatar samar da aikin yi da kuma hukumar kula da tsafta da lafiyar abinci da magunguna ta kasa wato NAFDAC tuni sun fara aiki gadan-gadan don lalubo yadda wannan kudurin zai cika.

Gwamnan yace babban makasudin samar da kasuwar shine ta yadda za’a samo hanyoyin da za’a habaka sana’ar har ma a rika fitar da kilishin a kasashen waje domin samun kudin shiga ga jihar da kuma aikin yi ga dumbin matasa.

A nasa jawabin shugaban kungiyar Alhaji Muhammad Mujitaba ya godewa gwamnan sannan kuma ya bashi tabbacin goyon baya.

You may also like