Gwamna Shettima Ya Bada Umarnin Daukar Ma’aikatan 300 Da Suka Kammala Jami’a Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya bawa hukumar kula da ma’aikatan jihar da ta dauki mutane 300 aiki wadanda suka gama makaranta.

Za a dauke su aikin ne daga cikin mutanen da suka kammala karatun jami’a, a fannoni daban-daban da suka fito daga kananan hukumomin jihar.

Shettima yabada wannan umarni ne lokacin da yake raba takardar sheda ga wasu matasa 10 da gwamnatin jihar ta dau nauyinsu, wajen samun horo a fannin samarwa da kuma rarraba hasken wutar lantarki a makarantar horar da ma’aikatan wutar lantarki ta kasa.

Gwamnan ya umarci shugaban ma’aikatan jihar da yau dauki matasan da suka kammala horon aiki, a ma’aikatun da suke aikin sake gina wuraren da rikicin Boko Haram ya lalata. 

Gwamnan yace za a dauki matasan aiki ne daga cikin guraben aiki 300 da yabada umarnin a dauki matasan da suka kammala jami’a ba tare da aiki ba.

An samu gurbin ma’aikata 300 ne, saboda nasarar da aka samu wajen tantance ma’aikatan jihar, inda aka gano ma’aikatan bogi sama da dubu goma da suka shafe kusan shekaru 20 suna karbar albashi daga gwamnatin jihar. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like