Gwamna Shettima Ya Roƙi Majalisa Da Ta Mayar Da Sanata NdumeGwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya Roƙi majalisar dattawan ƙasar ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Mohammed Ali Ndume.
Gwamna Shettima, wanda ya jagoranci sarakuna da dattawan jihar domin kai ziyara ga shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki, ya ce bai kamata a dakatar da Sanata Ndume ba musamman ganin irin rawar da yake takawa wurin kawo karshen kungiyar Boko Haram da kuma wakilcin da yake yi wa jihar na gari a majalisar dokokin.
Wata majiya da ke kusa da gwamnan ta shaida wa BBC cewa, Dakatarwar da majalisar dattawa ta yi wa Sanata Mohammed Ali Ndume ba karamin koma-baya za ta jawo mana ba; kar ka manta kusan babu dan majalisar da ke taka rawa wurin ganin an murkushe Boko Haram kamarsa. Ndume na cikin kwamitin tarayya da ke fafutikar ganin an sake gina arewa maso gabashin Nijeriya.”
A cewar majiyar, gwamna Shettima ya gana da Saraki da mataimakinsa Ike Ikweremadu da ‘yan majalisar dattawa daga arewacin kasar, duk dai da zummar rarrashin su su janye dakatarwar da suka yi wa Sanata Ndume.

You may also like