Gwamnan jahar Akwa-Ibom Emmanuel Udom ya kori malaman makaranta guda 5000 bayan da yace ya gano wata badakala a yadda ake daukan malamai a jahar, inda ya ce akwai wasu mutane da ke bayarda takardar daukan aiki ta jabu ga mutanen da basu cancanta su zama malamai ba.
A watat sanarwa da ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa duk wani yunkurin gwamnantinsa na ta gyara al’amarin ya ci tura, saboda matsalar ta samo asali ne tun daga ginshiki. A don haka ne babu abun da za su iya illa su kori malaman daga aiki gaba daya.
Ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta lankwasu ba wajen tabbatar da cewa ta yanke irin hukuncin da a karshe shi zai zamewa mutanen jahar alkhairi.
Ga malaman da aka kora, ya bukace su da su kara neman aiki, idan har sun cancanta, toh a wannan karan za’a duba su da kyau, kuma a kara daukar su aikin.
Ya ce gwamnatinsa ta bankado wasu mutane da ke buga takardun daukar aiki da takardun shedar gama makaranta na jabu akan makudan kudade kamar naira 150,000 zuwa 200,000.
Gwamnan ya yi watsi da wadanda ke surutu akan al’amarin inda ya ce kila su ke rike da takardun jabun.