A kokarin sa na habbaka harkar ilmi a jihar sa, Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya ware magudan kudade har sama da naira miliyan dari biyu (N200,000,000) domin biyan kudin makarantan daliban jihar Bauchi dake karatu a jami’ar Igbinedion dake Okada dake jihar Edo wanda gwamnatin da ta gabata ta kai su karatu.
Gwamna M.A ya biya kudin karatun daliban ne na shekaran 2015/2016 da kuma 2016/2017, a karkashin wata yarjejeniya wanda daliban za su karanta fannin kiwon lafiya da hada magunguna da kimiya.