Gwamnan Bauchi Ya Kai Ziyarar Gani Da Ido Inda Ake Aikin Hako Man Fetur A Jihar 



Gwamnan jihar Bauchi Barista M.A Abubakar ya kai ziyara ta musamman wurin da aka fara aikin hako mai a garin Alkaleri.

Gwamna a jawabin sa ya yi godiya ga Allah sannan ya sake mika godiyar sa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa soma aikin hako man da aka yi. Kuma ya bukaci Hukumar NNPC da kamfanin dake aikin man da su samar da aiyuka ga matasa yayin gudanar da aikin su, su kuma mutanen yankin su tabbatar sun ci gaba da bada hadin kai ga masu gudanar da wannan gagarumin aiki. 
Gwamna M.A Abubakar ya kuma ja hankalin al’ummar dake wannan yanki da su kara godiya wa Allah (SWT) da ya kawo wani arzikin da ba Jihar Bauchi kadai ba, arziki ne na kowa baki daya don haka su cigaba da bada gudumawar su da goyon bayan su saboda wannan aiki ya yi nasara. 
Ya kuma gargadi mutanen yankin da kar su taba wani abu da suka gani cikin gonakan su ko filayen su, kuma ya sake gargadin su da kar su yarda da duk wani sojan gona da zai zo ya sayi fili ko gonakinsu. Wannan Hukuma da kamfani suna kan binciken iya filayen da suke bukata, bayan sun gama za’a nemi wadanda filayen/gonakin su ya shiga cikin aiyukan.
A bangaren masu aiki hako mai kuwa, sun yaba da yunkuri, gudumawa, hadin kai, goyon baya da suke samu daga Gwamnatin Jiha da al’ummar  da suke yankin. Sannan sun jinjinaea Gwamna, kuma suka ce da tuntuni a kudancin Najeriya an sami Gwamna irin sa da ba’a sami matsalar ‘yan ta’adda masu fasa bututun mai ba. Kuma sun bada tabbacin za su dauki ‘yan asalin wannan yanki da arziki ya bullu daga wajen.
A bayanin sa na godiya Hakimin yankin, ya gode wa Gwamna ne da ya yi tattaki ya zo don nuna goyon bayan sa da wannan gagarumin nasara da aka samu a wannan yanki nasa. Kuma ya bada tabbacin cewa mutanen yankin sa masu biyayya ne, kuma suna shirye wajen bada gudumawar su da goyon bayan su wajen ganin wannan aiki yayi nasara.

You may also like