Gwamnan Bauchi Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Mai Daukan Sa Hoto Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan kawun daya daga cikin ma’ikatansa Shahruddeen Mu’azu Galaje, bisa rashin kawunsa Alhaji Abdullahi Sani Galaje.

Shahruddeen Mu’azu shine mai daukar hoton Gwamna Muhammad Abubakar.

Mataimakin gwamnan na musamman kan harkokin sadarwa Shamsuddeen Lukman Abubakar ne ya sanar da cewa gwamnan ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan fadar  gwamnatin, Alhaji Abdu Sule Katagum.

Haka zalika Gwamnan ya samu tarba daga Galajen Bauchi, Alhaji Adamu Abba tare da Mai Gudumar Galaje, Alhaji Abdu Shittu a madadin iyalan marigayin.

Daga karshe ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, tare da addu’ar Allah Ya kyautata makwancinsa.

You may also like