Gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abubakar ya kammala biyan diyyar gidajen da aikin fadada hanyar CBN roundabout zuwa Railway roundabout zai shafa.
Idan dai ba’a manta ba Gwamnatin Bauchi ta kaddamar da bayar da aikin hanyar mai tsawon kilomita 4.5 tun a watan Disambar bara amma rashin kammala biyan kudaden diyyar gidajen da aikin zai shafa tasa ala tilas aikin ya dakata.
Sai dai maitaimakawa Gwamnan a fannin sadarwa, Alhaji Shamsuddeen Lukman a wata sanarwa yace Gwamnan ya kammala biyan kudaden diyyar gidajen da za’a rushe kuma tuni aikin fadada hanyar ya cigaba.
Ana sa ran za’a samu saukin wahalhalu da cinkoson ababen hawa idan aka aka kammala aikin.