Gwamnan Bauchi Ya Taya Shugaba Buhari Murnar Cika Shekaru 75 A madadin al’ummar jihar Bauchi, gwamnan jihar Barista Muhammad Abdullahi Abubakar yana taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa, wanda a yau ya cika shekaru 75 da haihuwa. 

A wata takarda da mataimakin gwamnan na musamman a harkokin sadarwa Shamsuddeen Lukman Abubakar ya rabawa manema labarai, ya ce gwamnan ya taya shugaban kasa murna ne a shafukan sada zuntarsa na Facebook, Twitter, Instagram, inda ya bayyana rayuwar shugaban kasa a matsayin sadaukarwa wajen ganin ya samar da canji a rayuwar al’umma.

Gwamnan, ya kara bayyana cewa, jajircewar shugaban kasa ya kai kasar nan ga matsayi da ‘yan Nijeriya ba su yi tsammani ba, don haka ya bayyana aniyarsa da na ‘yan jiharsa na cigaba da ba shi hadin kai don samar ingantaciyar gwamnatin da jama’a za su yi dogaro da ita. 

You may also like