Gwamnan Bauchi Ya Ziyarci Matar Da Ta Haifi Ƴan HuɗuGwamnan jihar Bauchi a jiya Talata ya kai ziyara ta musamman ga Hajiya Fuzaimatu wato matar da ta haifi ƴan huɗu a farkon wannan watan. Gwamnan wanda mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Shamsuddeen Lukman ya wakilce shi, ya kawo ziyarar ne babban asibitin Azare domin duba lafiyar mejegon da jariranta tare da tallafa musu.

Ziyarar wadda tana daga cikin ziyarce-ziyarcen da mukarraban gwamnatin suke yi tun bayan kafa sabuwar gwamnatin, an baiwa mejegon tallafin kayan abinci da sauransu. Inda aka bada tallafin a gaban mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai, Muhammad Nuruddeen da mijin matar da kuma wasu daga cikin ma’aikatan asibitin.

Saidai jami’an asibitin sun tabbatar da cewa uku daga cikin jariran sun rasu yayin da dayan da yake a raye yake halin rai kwakwai mutu kwakwai. Sun tabbatar da cewa jariran bakwai ni ne.

                  

   

A madadin iyalan, mahaifin jariran Malam Sa’idu ya mika godiyarsa ga gwamnan da mukarrabansa da sauran jama’a. Yayin da ita kuma mejegon Fuzaimata ta fashe da kuka saboda farin ciki, inda ta yabawa gwamnan kan nuna damuwarsa gare su. Ta kara da cewa ba za ta taba mancewa da alherin da gwamnan ya yi mata ba.

A yayin mika ta’aziyya da taya murna a madadin gwamnan, Shamsuddeen Lukman ya bayyanawa iyalan cewa su dauki hakurin jure rashin jarirai ukun cikin hudu da suka haifa. Ya kuma umarci ma’aikatan asibitin da su baiwa mejegon da jaririn da ya rage kyakkyawar kulawa.

Idan har za a iya tunawa tun bayan kafa wannan sabuwar gwamnatin ta Bauchi, manyan mukarrabanta suke kai ziyara asibitotci daban-daban dake fadin jihar domin bada tallafi ga marasa galihu.

You may also like