Wannan karon gwamnan babban bankin ya yi amfani da hujjar cewa bai dawo daga tafiyar da ya yi kasar waje ba. Amma masana harkokin kudi na cewa a yi masa uzuri, kwararru a fanin siyasa na ganin a kwai abin da ke tsorata shi.
Tun a ranar 15 ga watan Disamba ne Majlalisar ta aike wa Emefiele da gayyata domin ya kara yi mata bayani akan manufar bankin kan sauyin fasalin kudin kasar ciki har da takaita yawan kudaden da mutum zai iya cirewa a asusun bankuna.
To sai dai zaman bai yiwu ba, saboda an aikewa Majalisar wasika cewa Gwamna Emefiele ba ya kasar. An karanta wasikar a zaman da aka yi jiya Talata, wadda ke dauke da sa hannun mataimakin gwamnan CBN, Edward Adamu, da ke cewa Emefiele bai dawo kasar ba har yanzu.
Hakan ya sa masanin harkokin diflomasiya da zamantakewar dan Adam, kuma malami a Jami’ar Abuja Dakta Farouk Bibi Farouk, cewa dole ne Emefiele ya ji tsoron fuskantar Majalisar domin bai tuntubi Majalisar ba kafin ya dauki matakin da ya dauka akan sauya fasalin kudi da kuma yawan kudaden da mutum zai iya cirewa a asusun banki.
Farouk ya ce akwai badakalar da ake ta bincike akan sa saboda haka zai ji tsoron fuskantar Majalisar.
Shi kuwa kwararre a fannin tattalin arziki, Ahmed Iliyasu Sardaunan Misau, ya na ganin kamata ya yi Majalisar ta ciza ta hura, tunda an bada hujjar rashin zuwan Emefiele.
Dan Majlisa mai wakiltar Birnin Kudu da Buji a Jihar Jigawa, Magaji Da’u Aliyu, wanda shi ne ya kawo kudurin gayyatar Emefiele a gaban Majalisar ya ce doka ta ba Emefiele dama ya nemi shawarar Majalisa kafin ya yi wani tsari da zai shafi kasa baki daya, amma bai taba zuwa Majalisar ba.
Magaji ya ce yin haka ya karya dokar kasa da kuma dokar da ta kafa babban Bankin kasar CBN.
Majalisar ta sake ba Emefiele dama ya bayyana a gabanta a ranar Alhamis, za kuma mu dawo da kawo muku abin da ya faru.
Saurari cikakken rahotan Medina Dauda: