Gwamnan farar hula na farko a jihar Adamawa ya mutu


Hoto:The Cable

Saleh Michika gwamnan farar hula na farko a jihar Adamawa  ya mutu.

Michika ya mutu a Cibiyar Kula Da Lafiya Ta Tarayya dake Yola bayan ya yi fama da jinya ya rasu ya na da shekara 77 da haihuwa.

Macaulay Hunohashi, mai bada shawara na musamman kan kafofin yada labarai ga gwamna Bindow na jihar Adamawa ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya mutuwar Michika a ranar Lahadi.

An zabi Michika a matsayin gwamna karkashin jam’iyar NRC.

 Ya kuma mulki jihar Adamawa daga watan Janairu na shekarar 1992 zuwa watan Nuwamba na shekarar 1993.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like