Gwamnan jihar Adamawa yayi barazanar barin jam’iyar APC


Bindow-Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa jibrilla Bindow ya koka kan yadda gwamnatin tarayya take nade-nade da kuma aiwatar da aiyuka da suka shafi jihar,inda yayi gargadi cewa shida mukarrabansa za’asa su dole su bar jam’iyar APC. Idan har ba a saurari ƙorafinsu ba.
Shugaban ma’aikata na gwamnan Andulrahman Jimeta yai wannan ƙorafi, a gaban gwamnan ba tare da gwamnan yace komai ba,lokacin da yakewa tawagar wakilai daga sakatariyar jam’iyar APC ta ƙasa jawabi, wadanda suka zo jihar dan gudanar da ƙaramin taron jam’iyar reshen arewa maso gabas.
Tawagar wacce Abdulƙadir Jajere yake shugabanta, sunje fadar gwamnan ne don su sanar dashi irin tsare-tsaren da sukayi na yin zaɓen cike gurbi a shiyar sakamakon nadin mukamai da akayi a Adamawa.
“Mu anan muna da biyayya, amma a faɗawa shugabancin jam’iya cewa biyayya ma tana da ƙarshe, kasancewa cikin jam’iya zabi ne kai ko addini kana da damar ka canza matukar aka takura maka” yace
Jimeta yace gwamnatin tarayya ta nada muƙamai da dama,batare da tuntubar gwamnatin jihar ba, yawancin waɗanda aka naɗa gwamnatin ta Adamawa bata sansu ba.
Abin takaici ne ace babu bambanci tsakanin jihar da jam’iyar adawa take mulki da kuma Adamawa inda APC take mulki wajen tuntuɓar gwamnati kafin a bada muƙami.
“Wasunsu bamu sansu ba,ba kuma a tuntuɓe mu ba kafin naɗin nasu”
Babban mai taimakawa gwamnan yace koda wasu aiyukan da yakamata ayiwa jihar wadansu da suke Abuja sun karkatar dasu.
Da yake yiwa tawagar jawabi gwamna Bindow yayi amfani da tattausan lafazi. Inda yanuna goyon bayansa ga kwamitin don su gudanar da aikinsu lafiya.
Gwamna Bindow na da dabi’ar wakilta shugaban ma’aikatansa yayi magana a madadinsa matukar maganar kan iya kawo ruɗani.
Koda a kwanakin baya sai da shugaban ma’aikatan yayi ikirarin gwamnatin jihar zata goyi bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a zaɓen 2019.

You may also like