Gwamnan Jihar Indiana Micheal Pence, ‘dan ra’ayin rikau na jamiyyar Republican, wanda shine Donald Trump ya zaba a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban kasa, a jiya Talata ya bayar da dalilan da yasa yake ganin sune suka dace su jagoranci Amurka.
Pence dan shekaru 57 da haihuwa yayi jawabin da ya dauki hankulan jama’a a rana ta uku wajen wannan taron, wato kwana guda bayan wakilai suka zabi wanda zai tsaya takara a karkasahin tutar jamiyyar ta Republican.
A cikin jawabin sa wajen taron Pence yace ya shirya fadawa Dubun dubatan Amurkawa ta gidan talabijin cewa gwamnatin da Trump yake fatar ganin ya kafa, ita ce gwamnatin da zata jaddada ci gaban Amurka da Amurkawa, bayan kasar tasha fama da manufofi marasa inganci da mulki mara kyau wanda yasa kasashen duniya suka yi rauni a harkokin Amurka.
Tun a cikin shekarar 1950 wannan ne karon farko da wani hamshakin attajiri wanda bai taba rike ko wane irin mulkamin siyasa ba ace ya zamo dan takara a karkashin duka fitattun jamiyyun nan guda biyu, wato ko dai Republican ko kuma Democrat.