Gwamnan Jihar Kogi Ya Kori Sakatarorin Dindindin Guda 8 Da Ma’aikata 1774



Gwamnatin Jihar Kogi ta tabbatar da yi wa wasu sakatarorin dindindin guda 8 ritaya, da wasu daractoci tare da sallamar wasu ma’aikatan Jihar da yawansu yakai 1,774 

Takardar sallamar ma’aikatan da ke dauke da sa hannun Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Mrs Deborah Ogunmola da kuma sa hannun shugaban hukumar daukar ma’aikata na Jihar Mr Ado Shaibu, inda aka rabawa manema labarai kwafin takardar.

Wasu daga cikin sakatarorin da abun ya shafa sun bayyana wa manema labarai cewa za su dauki matakin da ya dace na shari’a.

A nata bayanin da ta ke kare matakin da Gwamnatin ta dauka na korar ma’aikatan mai watsa labaran Gwamnan Jihar Kogi Mrs Petra Akinti-Onyegbula ta ce, an dauki wannan matakin ne domin tsaftace ma’aikatan Jihar “an yi wa sakatarorin ritaya ne saboda sun cika shekarun aikinsu, wasu kuma daga cikin ma’aikatan sun kure matakin aikinsu.” A cewarta 

Mai magana da yawun gwamnan ta ci gaba da cewa daractocin da aka sallama kuma sun cika wa’adin aikinsu na shekara takwas a mukamin na darakta wasuma harsun wuce, amma har yanzu ba mu fitar da cikakken adadin yawan daractocin da aka sallama ba domin an yi musu wata jarabawa tare da tantance su a ranar 12 ga watan Disambar shekarar da ta gabata wanda har yanzu sakamakon jarabawar bai fito ba wanda sai ya fito ne za mu san yawan daractocin da aka sallama ” 

Mrs Petra ta ci gaba da cewa daga cikin ma’aikatan 1,774 da aka sallama 1,667 takardun bogi gare su sai kuma 107 an same su da laifin rashawa da zamba wanda wani shirin tantance na’aikata da aka gudanar a shekarun 2016 da 2017 suka nuna

You may also like