Gwamnan Jihar Taraba Yace Bashi Da Hannu A Kisan Da Akayiwa Fulani A Yankin Mambila 


Gwamnan jihar Taraba , Darius Ishaku ya nisanta kansa daga zargin da ake masa na cewa yana da hannu a kisan kare dangi da ake yiwa Fulani a yankin Mambila dake Jihar. 

Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya Lahadi ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Emanuel Bello, yace  rahoton dake cewa gwamnan ya bada umarnin da a yiwa Fulani kisan kare dangi ” Ba gaskiya bane kuma  wadanda suke yada karyar basu da cikakken masaniya akan abinda ya faru.” 

Yayi Allah wadai da rikicin da yafaru tsakanin Fulani da kuma yan kabilar ta Mambila a karamar hukumar Sardauna dake jihar. 

” Dole ne ayi Allah wadai da zubar da jini a ko ina yafaru,bawai sai kawai wasu rukunin mutane sun nuna cewa su abin ya shafa ba,” Ishaku yace.

Sanarwar ta kalubalanci masu sukan gwamnan kan su nuna wata takarda, kaset ko bidiyo da aka nada dake nuna  yadda gwamnan ya bada umarnin.

Bello ya bayyana masu zargin gwamnan a matsayin mutane da suka kasa fahimtar me ake nufi da kisan kare dangi. 

Gwamnan yakara da cewa a jihar Taraba dukkanin rayukan mutanen jihar suna da muhimanci a gurin mu shiyasa  ako da yaushe yake kira da a zauna  lafiya kuma takensa kenan cewa “ku bani zaman lafiya nikuma na kawo muku aiyukan cigaba .”

A kwanakin bayane dai aka samu rikici tsakanin Fulani da kabilar Mambila a garin Nguroje kafin daga bisani rikicin ya watsu a garuruwan dake yankin. 

You may also like