Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Allurar Rigakafin Cutar Shan’inna  a Rano


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya jagoranci kaddamar da allurar rigakafin shan’inna na watan Oktoban bana a karamar hukumar Rano dake jihar.
Cikin wadanda sukayiwa Gwamnan rakiya zuwa karamar hukumar ta Rano sun hada da yan Majalisar Zartarawar jihar, da mataimakin Gwamnan da Kakakin majalisar dokokin jihar da mambobinsu da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin kiwon lafiya a jihar.
Gwamna Ganduje ya kuma yi amfani da damar wajen kaddamar da bikin ranar wanke hannu ta duniya wacce hukumar lafiya ta duniya, WHO ta tsaida duk ranar 15 ga watan Oktoban kowace shekara.

Gwamnan da tawagarsa sun wanke hannayensu a gaban jama’a domin kara masu kwarin guiwa da nusar dasu fa’idar dake tattare da wanke hannuwa da kula da kiwon lafiya musamman bayan amfani da bandaki.

You may also like