Gwamnan Katsina Ya Nanata Kudirinsa Na Bunkasa Noman Rani a Jihar



Gwamnan Jahar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya kudiri aniyar bunkasa harka noma ta hanyar tallafamawa manoman da basu kwarin gwiwar daomin  habbaka tattaalin arzikin jahar Katsina da kasa baki daya.

 

Da yake jawabi a wajen kaddamar da noma ranin shinkafa a madatsar ruwa ta garin Jibia ya ce gwamnatn jahar ta bada kwangilar gyara wadansu daga cikin madatsun ruwa da take da su domin bunkasa noman rani. 

Madatsun ruwa sun hada da Daberam da Ruwan Sanyi da Masari, da Kwanar Are da Sonkaya da Yartsaku da Makera da kuma Bakori; wasu ma daga cikin madatsun ruwa ana gab da kammala aikinsu domin fara noman ranin.
Gwamnan ya kara da cewa domin karawa manoman ranin kwarin gwiwa an sawo fanfon ban ruwa guda dari shidda da ashirin akan kudi naira miliyan ashirin. Kuma nan gaba kadan za a raba su ga manoman rani a jahar, kuma shirye shirye sun yi nisa wajen samawa manoman rani taraktoci dari ukku da irin da kuma samar da takin zamani domin bunkasa harkar noma rani a jahar.
Masari ya cigaba da cewa Gwamnatin jahar Katsina na cigaba da tuntuba domin ganin ta kafa cibiyar bincken shinkafa a garin Daudawa da kuma  yin babbar ma’ajiyarta a garin Dandume. Yanzu haka maaikatar gona ta jahar Katsina na cigaba da tantance ainihi manoma da kuma yawan gonakinsu da yanayi kasa da irin hatsin da take bukata a shuka a duk fadin jahar. 
Bikin kaddamar da noman ranin shinkafa wanda ake sa ran manoman dubu ashirin ne za su noma shinkafa kadada dubu dari,hadin gwiwa ne da Babban Banki Kasa wato (CBN) wanda ke da taken Hannun Amsa Hannun Maidawa (Anchor Barrower For Rice Production)ya samu halartar mataimakin Gwamnan Jahar Katsina Alhaji Mannir Yakubu, wanda kuma shi ne Kwamishinan Noma, Wakilan Gwamnan Babban Banki Kasa da Shugaban Banki Manoma da Kakakin Majalisar Dokoki Aliyu Sabi’u Muduru da kwamishinoni da masu ba Gwamna shawara.

You may also like