Gwamnan Kebbi Ya Aurar Da ‘Yan Mata Marayu Dake Zaune A Gidan Marayun JiharA ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya aurar da ‘yan mata marayu guda hudu dake gidan marayun jihar. Auren wanda aka daura shi a fadar Sarkin Gwandu, Gwamna Bagudu shi ya zama Waliyin amaren wadanda tuni sun kammala karatunsu tare da koyon aikin hannu.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su kasance masu tallafawa marasa galihu sannan kuma su kasance masu sanya ido a yankunan su da yaransu don magance matsalar shaye-shaye a tsakanin matasa. Inda ya kara da cewa Sarakunan gargajiya na iya kokarin su don ganin an fara kawar da matsalar shan kayan maye a cikin gari.

Naira dubu 40 aka biya a matsayin sadakin auren Gaddafi Muhammadu Fana da Zara’u Musa ta hannun waliyinsa Salisu Fana, yayin da Lawal Yahaya Mera wanda ya auri Zainab S.T Bello, ya biya naira dubu 20 a matsayin sadaki ta hannun waliyinsa Alhaji Bashir, Dan Malikin Zauro.

Mallam AbdulMuminu Abdulmumin Aguji wanda ya zabi Rabi’atu A. Adamu a matsayin matarsa, shi ma ya biya naira dubu 40 a matsayin sadaki ta hannun Waliyinsa Ibrahim Abdllahi Kofar Guga Katsina, yayin da aka biya dubu talatin a matsayin sadakin auren Nafi’u da Zainab ta hannun Waliyinsa Alh. Idris Umar Magajin Bunga. 

Wasu daga cikin masu fada a ji na jihar Kebbi, da suka hada da mataimakin Gwamna, Kanal Ismaila Yombe Dabai, mataimakin kakakin majalisar jihar, kwamishinoni, sakataren gwamnatin jihar, walikin kwamishinan ‘yan sandan jihar, daraktan hukumar SSS na jihar, tsohon ministan albarkatun ruwa, Isah Muhammad Argungu, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Attahiru Maccido da sauran su na daga cikin wadanda suka halarci daurin auren. 

Babban Limamin masallacin Juma’a na Wala, Malam Ahmed Rufa’i, babban limamin masallacin Juma’a na fadar Sarki, Malam Muhammadu Lawali, Malam Salisu Fana da na masallacin Juma’a na Yar-Yara, Liman Laba ne suka jagoranci addu’ar daurin auren.

Bayan gudanar da walima a gidan Dakta Hali Bala, daga bisani uwargidan gwamnan ta yi wa amaren wasiyya game da rayuwar zaman gidan miji.

You may also like