Gwamnan Kwara ya yi tayin miliyan ₦5 ga duk wanda yake da bayani kan yan fashin da suka kai hari garin OffaGwamnan jihar Kwara,Abdulfatah Ahmad, ya yi tayin kudi har naira miliyan ₦5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama yan fashin da su kai fashi a garin Offa dake jihar.

A ranar Alhamis yan sanda da kuma mutane garin da dama sun rasa rayukansu bayan da wasu yan fashi da makami suka  kai hari kan wasu bankunan kasuwanci biyar dake garin.

Yan fashin sun tsare hanyoyin shiga garin daga garin daga  Osogbo da kuma Ilorin a lokacin da suke aikata ta’asar.

A wata sanarwa ranar Asabar, Muyidin Akorede, mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai ya habarto Ahmad na cewa duk wanda yake da wani bayani mai amfani da zai kai ga kama yan fashin to ya tuntubi rundunar yan sandan jihar ta wandannan nambobin layukan wayar tarho -0803 739 1280 da kuma 0803 236 5122.

Gwamnan ya bawa mutanen da za su iya samar da bayanan tabbacin cewa za a  kare lafiyarsu ta yadda babu wani abu da zai same su sanadiyyar taimakawa jami’an tsaro da za su yi domin a kama maharan.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin maharan sun fuskanci hukunci.

You may also like