Hukumar kula da mahajjata a Najeriya ta musanta zargin da ake kan gwamnatin Tarayya ta dauke sharadin canji akan Mahajjatan bana.
A cikin wata sanarwa, Kakakin hukumar Uba Maina ya ce gwamnatin Najeriya ta dauki mataki kan mahajjatan bana tun kafin a kaddamar da sabon tsarin canji a yanzu.
Wannan dai ya janyo cece-kuce tare da sukar gwamnatin shugaba Buhari bayan kin janye tallafin canjin ga ‘Yan kasuwa masu shigo da magani da kuma Dalibai da ke karatu a kasashen waje.
A yau litinin ne ake shirin soma jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga kasar zuwa kasar Saudiya.