Gwamnati Ta Fara Biyan Tallafin 5000 Ga Wadanda Aka Tantance



Gwamnatin tarayya ta fara biyan Tallafin Naira 5000 ga  marasa galihu a jihohi hudu daga cikin guda Tara na rukunin farko da aka tsara farawa shirin da su.
Mai Ba Mataimakin Shugaban kasa shawara kan Harkokin Yada Labarai, Laola Akande ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka amfana da shirin sun fara karbar 5000 tun a makon da ya gabata wadanda suka hada da jihohin Bauchi, Borno, Kwara. Ya ce sauran jihohin da za a fara biya sun hada daCross Rivers, Niger, Kogi, Oyo, Ogun da Ekiti.

You may also like