Gwamnati Ta Fara Tantance Malamai 200,000 Da Za’a Dauka Aiki – Osinbajo


Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa tuni gwamnati ta yi nisa wajen fara tantance mutane  200,000 daga 500,000 na rukunin farko na malamai da gwamnati ta tsara dauka aiki a cikin wannan shekara.
Ya ce kafin karshen wannan wata za a kammala aikin tantancewar inda ya nuna cewa yana daga cikin shirin nan na N-Power na Tallafin gwamnati inda ya nuna cewa za a fara aiwatar da shirin ne a wasu kebantattun jihohi.
Haka nan kuma, Mataimakin Shugaban ya nuna cewa a cikin wannan wata ne gwamnati za ta fara aiwatar da shirin ciyar da daliban Makaranta wanda aka kebe Naira Bilyan 500 don cimma nasarar shirin.

You may also like