Gwamnati Ta Gargadi Masu Laifin Kin Biyan Haraji Kan Wa’adin Bayyana Kadarori Shugaban Hukumar Tara Haraji ta kasa, Mista Babatunde Fowler ya gargadi masu laifin kin biyan haraji kan su yi amfani da damar da gwamnati ta ba su na bayyana adadin kadarori da kudaden da suka mallaka tare da biyan harajin da ake binsu kafin wa’adin garabasar ya cika.

Ya ce, gwamnati ba za ta kara wa’adin ba wanda zai cika a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2018 inda ya nuna cewa duk wanda ya bari wa’adin ya cika ba tare da biyan harajin ba zai dandana kudarsa.

You may also like