A ranar 28 ga watan Yunin 2014, Ministan babban birnin tarayya Abuja, Sanata Bala Muhammad, ya umarci Kwamishinan ‘yan sanda na birnin tarayya, da ya kama tare da gurfanar da duk wanda aka kama yana tuka babur din nan mai tsananin gudu a tsakiyar birnin tarayya Abuja.
Wannan umarni ya biyo bayan, wani bayani da jami’an tsaro suka bayar na cewar, wadan da suka kai hari a EMAB Plaza dake unguwar Wuse II a babban birnin tarayya Abuja, sun yi amfani da irin babur dinanna mai tsananin gudu.
Tun da jimawa daman aka haramta amfani da Baburan hawa a birnin Abuja, amma kuma masu amfani da babur din nan mai tsananin gudu kirar zamani, suna cin karensu da babbaka, domin suna yin guje guje ba tare da doka ta yi aiki a kansu ba.
Wannan umarni, an baiwa kwamashinan ‘yan sanda na lokacin a wasikar da Ministan ya aike masa a ranar 27 ga watan Yunin 2014, kuma Sakataren din-din-din John Chukwu ya sanyawa hannu, yana mai cewar, dokar hana amfani da babura a cikin birnin Abuja tana nan a lokacin.
A saboda haka, wannan doka har yanzu tana nan kamar yadda wani jami’i a FCTA ya tabbatarwa Majiyar kuma har yanzu Ministan Abuja Muhammad Musa Bello bai ce an canza dokar ba.