Gwamnati Ta Maka Sanata Misau Kotu Kan Yi WaSufeto Janar KazafiGwamnatin tarayya ta maka Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Bauchi ta Tsakiya, Sanata Isah Misau kotu bisa laifin yi wa Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Ibrahim Idris kazafi na karbar toshiyar baki daga kwamishinonin ‘yan sanda don tura su wuraren aiki masu maiko.

Mai gabatar da kara a madadin Ministan Shari’a, Aminu Aliyu ya shaidawa wata kotun birnin tarayya cewa Sanata Misau ya zargi Sufeto Janar da karkatar da wasu kudade da aka ware don sayen motocin yin sintiri sannan kuma ya nada ‘yan kabilarsa na Nupe mafi yawan kwamandojin rundunonin ‘yan sandan kwantar da Tarzoma wanda a cewar mai gabatar da karar, duk wadannan zarge zargen karya ne.

You may also like