GWAMNATI TA SAKI BILYAN 750 A WANNAN MAKO DON GUDANAR DA MANYAN AYYUKA 



Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta tabbatar da cewa a cikin wannan mako ne gwamnati za ta saki Naira Bilyan 750 ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati don aiwatar da wasu manyan ayyukan raya kasa da ke cikin kasafin kudin 2017.

Ta ce, tun da farko gwamnati ta fara Sakin Naira Bilyan 450 bayan amincewa da kasafin kudin a watan Yuni inda ta ce manufar gwamnati ita ce na inganta abubuwan more rayuwa.

You may also like