Gwamnati Ta Sallami Malaman Kwalejin Fasaha Ta Auchi dake Edo State Su 13 Bisa laifin FasikanciGwamnatin tarayya ta sallami wasu malaman kwalejin kimiyya da fasaha ta Auchi da ke jihar Edo bisa samun da laifin yin fasikanci da dalibai mata da Zimmar  kara masu maki a jarrabawa.
Haka ma, gwamnati ta rage girma ga  wasu malaman kwalejin su 16 bisa laifin da ya jibinci fasikanci. Wannan mataki na gwamnati ya biyo bayan wani bincike ne da aka gudanar sakamakon wani rahoto da ya fallasa yadda dalibai maza ke tura ‘yan matansu su kwana da malamai don su samun damar cin jarrabawa.

You may also like