Gwamnati Ta Sanya Wa’adin Haramta Tallan magunguna Akan Tituna



A wani mataki na inganta harkar samar da ingantattun magunguna, Gwamnatin tarayya ta sanya ranar 1 ga watan Agusta na shekarar 2017 a matsayin ranar wa’adin dakatar da sayar da kowane irin nau’ukan magunguna a kan titinan kasar nan.
Shugaban Kungiyar Kwararru Kan Hada Magunguna na zamani, Elijah Muhammad ne ya sanar da haka inda ya nuna cewa bin matakin ya zama dole na kawo karshen yadda ake Jefa rayukan jama’a cikin hadari ta hanyar sayar da jabun magunguna.
Ya ce an tsara tattara masu sayar da magunguna a cibiyoyi na musamman ta yadda za a samun saukin sa ido a kan Harkokin sayar da magunguna inda ya nuna takaicinsa kan yadda mafi yawan masu sana’ar sayar da magunguna ba su da rajista kamar yadda doka ta tanada.

You may also like