Gwamnati Ta Yi Karib Haske Kan Matakan Rage Farashin Kayan Abinci 



Ministan Albarkatun Gona, Cif Audu Ogbeh ya bayyana cewa gwamnati ba ta da niyyar kayyade farashin kayayyakin abinci sai dai kawai za ta dauki mataki ne kan abubuwan da ke janyo tsadar abinci wanda ya hada da sufuri da kuma haraji da aka tsawwalawa  masu fataucin abincin.
Ya ce tuni kwamitin da gwamnatin tarayya ya kafa na ministoci ya rubutawa wasu jihohi inda wasu jami’ai kan rufe manyan hanyoyi suna karbar haraji ba bisa ka’ida ba ga masu fataucin abinci daga wani sashen kasar nan. Ya kara da cewa gwamnati za ta yi tanadi ta yadda za a rika amfani da jiragen kasa wajen jigilar kayayyakin abincin.

You may also like