Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Bayar da Shawarwari Kan Yaki da rashawa, Farfesa, Itse Sagay ya tabbatar da cewa a karshen wannan wata ne gwamnati za ta fara biyan mutumin nan da ya fallasa kudaden nan har Naira Bilyan 13 da aka gano wani gida da ke yankin Ikoyi a jihar Legas.
Ya ce mutumin zai samu Naira milyan 860 a matsayin kashi biyar na kudaden da aka gano kamar yadda gwamnati ta tsara. Ya kara da cewa dole za a shiryawa mutumin horo kan yadda zai sarrafa wadannan kudade don ganin bai salwantar da su a banza ba.