Gwamnati Za Ta Kwace Gidaje 22 Mallakar Ekwuremadu


Gwamnatin tarayya ta maka Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekwuremadu kotu inda ta nemi kotun ta mika mata wasu gidaje har 22 mallakar dan majalisar.

A cikin karar da gwamnati ta shigar a kotun ta nemi a mika mata gidaje 9 na Mataimakin Shugaban majalisar da ke Abuja sai kuma wasu gidaje biyu a birnin Landon, sai kuma gidaje takwas da ke Dubai sannan wasu gidajen uku da ke Amurka.

You may also like