Gwamnati Za Ta Yi Amfani Da Kuɗaɗen Abacha Wajen Tallafawa Talakawa


Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa za a tallafawa talakawa da Dala milyan 322.52 na kudaden da Tsohon Shugaban Kasa, Marigayi Sani Abacha a boye a bankuna Swiss wanda kuma aka mallakawa Nijeriya kudaden kwanan nan.

Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta ce tuni aka adana wadannan kudade a cikin wani asusu na musamman a Babban Bankin Nijeriya. Gwamnati tarayya dai ta kaddamar da wasu shirye shirye na tallafawa marasa galihu kai tsaye wanda ya hada da Naira dubu biyar biyar da ake ba su wasu magidanta.

You may also like