Gwamnati Zata Haramta Wa Likitoci Aiki A Asibitoci Masu Zaman KansuA zaman da majalisar ministoci ta gudanar a jiya Laraba a karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari, majalisar ta amince da daukar mataki na Haramtawa Likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati yin aiki a asibitoci masu zaman kansu ko kuma kafa tasu asibitocin.

Da yake karin haske kan zaman majalisar, Ministan Kiwon Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya ce an kafa wani kwamitin kwararru wanda zai duba sakamakon rahoton kwamitin Yayale Ahmed game da yadda za a inganta Harkokin kiwon lafiya a Nijeriya wanda aka kafa a zamanin mulkin Jonathan.

Haka kuma Ministan ya ce majalisar ministocin ta nemi al’ummar Nijeriya su kwantar da hankularsu game da barkewar cutar nan ta ‘ Monkeypox’ inda majalisar ta bukaci jama’ar kasa kan su kula da tsafta tare da kai rahoton duk wanda suka gani  da alamomin cutar tare da shi inda Ministan ya tabbatar da cewa an tanadi wasu cibiyoyi na musamman don tunkarar kalubalen cutar.

You may also like