Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta gudanar da bukukuwan cikar Shugaba Muhammad Buhari kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Ministan ya ce yin bikin ya zama dole saboda a nunawa ‘yan Nijeriya irin nasarorin da Buhari ya samu a tsakanin wadannan shekaru inda ya nuna cewa gwamnati na alfahari bisa matakan gaggawa da ta dauka na farfado da tattalin arzikin Nijeriya.