Shugaban Kungiyar Kwadago ta kasa, Kwamred Abdulwahab ya zargi gwamnatin APC da jefa ma’aikata cikin yanayin talauci ta yadda har an samu wadanda suka kashe kansu sakamakon kuncin rayuwa a cikin shekarar 2017.
Da yake isar da sakon sabuwar shekara ga daukacin ma’aikatan gwamnati da al’ummar Nijeriya, Shugaban kungiyar ya nuna cewa a shekarar da ta gabata, ma’aikata da ‘yan Nijeriya sun shiga cikin mawuyacin hali.