Gwamnatin Bauchi Ta Mika Sakon Ta’aziyya Kan Rasuwar Wazirin KatagunGwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Barista Muhammed Abdullahi Abubakar, ta sanar da sakon ta’aziyar ta ga masarautar Katagum da jama’ar Bauchi baki daya kan rasuwar Wazirin Katagum, Alh Sule Katagum.

A wata sanarwa da ta fito daga kakakin Gwamnan akan harkokin sadarwa Alhaji Shamsuddeen Lukman Abubakar, ya ce gwamnan ya kadu matuka da rasuwar Wazirin Katagum, daya daga cikin hazikan ma’aikatan kasa wanda ya bauta ma kasa a lokacin rayuwarsa. Gwamnan ya musalta Wazirin Katagum, da cewa Shi uba ne abun koyi ga kowa wanda yayi rayuwa cikin koyarwar addinin musulumci, 

Gwamna M.A Abubakar ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan sa da rahama ya bashi Jannatul Firdaus.

Marigayi Alh. Sule Katagum, uba ne ga Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Bauchi Arch. Alh Audu Sule Katagum.

You may also like