Gwamnatin Bauchi Ta Yaye Matasa 1400 Domin Aikin Tsaro


A wani kokari da gwamnatin jihar Bauchi take yi wajen ganin ta ceto rayuwar matasa ta hanyar sama musu aiyukan yi, a ranar Litinin din da ta gabata, hukumar nan ta inganta rayuwar mata da matasa (BACYWORD) ta kaddamar da wani sabon shiri da zai taimaki rayuwar matasan dake jihar.

Kimanin matasa 1,400 ne suka sami damar shiga cikin shirin wanda aka yi masa suna da ‘Zabgai Security Service Limited’, domin ya rika taimakawa wajen gudanar da aiyukan tsaro a ko ina a cikin faɗin jihar nan.

Wannan dai na daga cikin cika irin alkawuran da a ka dauka a yayin gudanar da yakin neman za6e a shekarar 2015 data gabata. Wannan shiri dai ba shi ne a karon farko da gwamnatin ta fara domin ci gaban matasan dake jihar.

You may also like