Gwamnatin Bauchi Zata Kawar Da Tsarin Karatun Mata Da Maza A Wuri Daya
Gwamnatin jihar ta ce dama wannan shirin dadadde ne, yanzu ne aka samu sukunin aiwatar da shi.

Makaranta dai wuri ne na bada ilimi da gyaran tarbiyya, da kuma cusa kyawawan dabi’u domin samun shugabanni nagartattu kuma abin koyi.

Wasu abubuwan juyayi sun faru a baya a daya daga cikin makarantun gaba da firamare a cikin garin Bauchi. Shekaru biyar da suka gabata wasu dalibai sun shirya yin aure a tsakaninsu, har ma sun biya kudin sadaki tare da raba goro, abinda ya sa gwamnatin wancan lokacin rufe makarantar.

Bugu da kari bayyanar wayar salula ta canza fasalin rayuwar dalibai da yawa, inda suke koyon munanan dabi’u.

Dakta Aliyu Usaman Tilde, shi ne kwamishinan ilimin jihar, ya ce hukumar zartarwar jihar Bauchi da ta kunshi Gwamna, kwamishinoni, da manyan jami’ansa ta amince da daukar matakin kafa makarantar mata zalla da maza zalla a duk fadin jihar, ko kuma a ware su gefe dabam-daban a cikin makaranta daya.

Kasancewar ita gwamnati ta shirya wa shirin ta hanyar tanadar da wuraren karatu da masu koyarwa a makarantun, ko me makarantu masu zaman kansu ke cewa kan sabon matakin? Malam Sai’du Dalhat Bawa, mai makarantar Ahlullahi Academy a garin Bauchi, ya ce sun yi marhabi da matakin.

Ga rahoton Abdulwahab Mohammed cikin sauti:

You may also like