Gwamnan jahar Borno Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnatin sa ta sauya shawara game da mayarda ‘yan gudun hijira garuruwan su a karshen watan Mayu.
Gwamnan ya ce hakan ya biyo bayan ci gaba da kai hare hare da ‘yan ta’addan ke yi musamman a yankunan da ke kusa da dajin Sambisa.
A shekarar da ta gabata ne gwamnatin jahar Borno ta yanke hukuncin rufe ilahirin sansanonin ‘yan gudun hijiran da ke jahar a karshen watan Mayu, domin a baiwa ‘yan gudun hijiran damar yin azumin Ramadan a gidajen su.
Sai dai gwamnan ya ce duba da ayyukan da sojoji ke yi a yankin Sambisa a kwanakin nan ya sa dole su sauya shawara.
Yayin da ya ke gabatar da jawabin sa a wajen taron kaddamar da wasu gine ginen da aka gyara bayan da aka ruguje su a rikicin, gwamnan ya ce burin su shine su tabbatar sun kare rayukan mutanen jahar.
A don haka ne ya ce ba za su mayar da ‘yan gudun hijiran ba har sai sun tabbatar dari bisa dari cewa an samu kwanciyar hankali, kuma mutane za su iya gudanar da rayuwar su ba tare da tsoro ba.