Ministar kudi ta Najeriya Misis Kemi Adeosun ta bayyana cewa, ba manufofin gwamnatin Buhari ba ne suka janyo matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta a kasar ba, inda ta ce, gwamnatin baya ce ke da alhakin halin da aka fada.
Ministar ta zanta da ‘yan jaridu bayan taron majalisar zartarwa da aka gudanar a ranar Larabar nan a fadar shugaban kasa, inda ta ce, matsalar tattalin arziki ba abu ne da ya afku a rana daya ba.
Ta ce, wannan matsala ta faro ne shekaru 6 da suka gabata inda aa dinga kashe kudade a Najeriya kan bukatun yau da kullum maimakon a gudanar da manyan aiyuka na cigaban kasa.
A yanzu kuma gwamnati mai ci na ta kokarin ganin ta warwa wannan matsala.
A yanzu dai Najeriya na fuskantar matsalar tattalin arziki.