Gwamnatin Faransa za ta rufe Masallatan kasar


 

 

Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa Cazeneuve ya bayyana cewa, a karkashin dokar ta baci da aka saka za su iya rufe dukkan Masallatan Juma’a da na Khamsu Salawat da ke kasar.

A karkashin dokar a makon da ya gabata an rufe Masallatan Juma’a 4, inda aka kuma bayyana alkaluma game da yaki da ta’addanci da aka fara tun shekarara 2015 a kasar.

Ya zuwa yanzu an rufe Masallatai sama da 20 a kasar kuma ana ci gaba da bincike a wuraren ibadar Musulmi.

Haka zalika an kama mutane 426 tare da kai 95 gidan kurkuku tun bayan kai harin birnin Paris.

A binciken da aka yi a gidaje dubu 4 an kwace makamai 600 wadanda 77 daga cikin masu hadari ne sosai.

Tun daga farkon shekarar 2015 zuwa yau an kori ‘yan kasashen waje 80 daga kasar tare da hana wasu 201 shiga.

Haka zalika an hana mutane 430 fita daga kasar sakamakon zargin suna da niyyar yin yaki tare da ‘yan ta’adda.

A matakan da aka dauka kan yanar gizo kuma an rufe shafuka 54 tare da hana amfani da adreshin e-mail 319.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Faransa ce ke da alhakin rufe Masallatai da shafukan yanar gizo a bincike kan ta’addanci daake yi.

A ranar 13 ga watan Nuwamban shekarar 2015 ne aka kai hare-haren bam a birnin Paris a wurare 6 daban-daban inda aka kashe mutane 130, wanda tun bayan wannan lamari aka saka dokar tabaci.

You may also like