Gwamnatin Filato Za Ta Share Wa Musulman Jihar Hawayensu


lalong22

 

 

Gwamnan Jihar Filato, Barista Simon Bako Lalaong, ya tabbatarwa Musulman jihar cewa gwamnati maici yanzu a jihar na nazarin dukkan koke-koken da suka gabatar mata don magancesu daya bayan daya.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da shugabannin Musulmin da suka kai masa gaisuwar sallah a gidan gwamnati da ke Rafeil Jos, a makon jiya.

Gwamnan wanda ya yaba da irin kyakkyawar goyon baya da hadin kai da al’ummar jihar ke ba shi, ya ce tuni gwamnatin ta samar masu da makeken filin makabarta don magance wahalhalun da suke fuskanta a lokacin da duk dan uwansu ya rasu, kuma ya umurci shugaban Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ya hanzarta share filin don baiwa Musulman damar fara amfani da shi.

Har ila yau, ya ce gwamnatin jihar ta samar wa Hukumar Alhazai ta Jihar Filato sabon ofishi a kan titin Bauchi, cikin garin Jos don saukake masu zirga-zirga a lokacin da su ke shirin tafiya Kasar Saudiya don sauke farali.

Game da makarantar Sardauna Memorial wadda Musulman jihar suka yi kukan gwamanatin da ta gabata ta danne masu hakkinsu a kai, ya ce gwamanati na yin kokari don ganin an magance matsalar.

Tunda fari, da yake magana a madadin al’ummar Musulmin jihar, mai martaba Sarkin Kanam, Alhaji Muhammad Babangida ya tabbatar wa gwamnan cewa Musulman jihar za su ci gaba da bashi kyakkyawan hadin kai da goyon baya, kana a ya ce a shirye suke su ba da nasu taimakon a duk lokacin da bukatar haka ta taso.

You may also like