Gwamnatin Iraki ta kwace makarantun FETÖ da ke kasar


 

Gwamnatin kasar Iraki ta karbe iko da makarantun kungiyar ta’adda ta Fethullah FETÖ da ke kasar inda za ta debi malamai ‘yan kasar su koyar a makarantun.

Tuni aka fara shirye-shiryen mika makarantun ga ma’aikatar ilimi ta kasar.

Makarantun na bayar da darussa a harshen Turanci amma kuma bisa tsarin koyarwar kasar Iraki.

Ana sa ran cewa, bayan an kammala karbe makarantun za a ci gaba da bayar da karatu a cikin harshen na Turanci.

Mahukuntan Iraki sun bayyana cewa, suna tattaunawa da ofishin jakadancin Turkiyya da ke Baghdad domin ganin an samar da sabon tsarin karatu a makarantun. Haka zalika game da daukar ma’aikata, Iraki da Turkiyya za su hadin gwiwa wajen tabbatar da wannan aiki.

A ranar 16 ga watan Oktoba ne ma’aikatar Ilimi ta Iraki ta fitar da sanarwar yunkurin kwace makaruntun na FETÖ.

Jakadan Turkiyya a Baghdad Faruk Kaymakcı ya sanar da cewa, yunkurinsu na shekaru 2.5 game da makarantun na FETO a Iraki ya fara bayar da sakamako mai kyau.

Kaymakcı ya ce, ma’aikatun Ilimi na Iraki da Turkiyya da kuma da kuma Asusun Ilimi na Ma’arif na ta zyartar juna don tabbatar da wannan shiri.

You may also like