Gwamnatin Jahar Bauchi Ta Haramta Gudanar Da Kowane Irin Taro a Fadin Jahar


bauchi

 

 

Wata takarda da gwamnatin jahar Bauchi ta fitar daga ofishin sakataren gwamnatin jahar mai dauke da kwanan wata 23 ga watan Nuwamba na nuna cewa gwamnatin ta hana ko wani irin taro ko gangami a fadin jahar.

Takardar ta bayyana cewa gwamnatin ta dauki wannan mataki ne a sakamakon barazanar rashin tsaro da jahar ke fuskantar.

Ta kuma bukaci jami’an tsaro da su tabbatar da kafuwar wannan doka.

Toh tunda gwamnatin ba ta tantance wani irin taro take nufi ba, abunda wasu ke tambaya shi ne, shin wannan haramci ya shafi taruka irin na aure ko walima ?

You may also like