Gwamnatin Nijeriya ta Kaddamar Da Shirin Da Zai Kawo Karshen Aurer Da Mata Kanana


child-bride

 

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kaddamar da shiri na musamman domin hana aurar da mata kanana da kare hakkokin su da kuma aiwatar da dokar da za ta hukunta masu tilasta musu auran.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tare da hadin gwiwar hukumar kula da yawan al’umma na Majalisar Dinkin Duniya ne suka jagoranci kaddamar da wannan shiri.

A sakamakon yawan korafe korafe da take samu, hukumar dake kula da yawan jama’a na MDD ta gudanar da bincike inda ta gano cewa kashi 60 na ‘yan mata a nahiyar Afirka, ana yi masu aure ne kafin su kai shekaru 18.

Tun a shekarar 2013 ne Nijeriya ta shiga jerin kasashen Afirka da suka amince da dokar hana aurar da mata da wuri, amma izuwa yanzu Jahohi 23 kawai suka aiwatar da dokar.

Kungiyoyin kare hakkokin mata a Nijeriya dai na ta kira ga gwamnatin da ta gaggauta daukar matakan hana aurar da mata da wuri a fadin kasar.

You may also like