Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana sanarwar tsige Malam Inusa Andu daga mukamin sakataren ilimi a karamar hukumar Kiyawa.
Wannan sanarwa na kunshe ne cikin wata takarda wadda jami’in yada labarai na ma’aikatar kananan hukumomi a jihar Alhaji Najib Umar ya rattaba wa hannu tare da mikata ga manema labarai cikin makon da ya gabata a Dutse.
Sanarwar ta umarci tsigaggen sakataren da ya mika duk wasu muhimman takardu da bayanai na ofishin ga shugaban ma’aikata na karamar hukumar.
Takardar ta bayyana cewa, wannan tsigewa ta fara aiki daga lokacin da aka bada wannan sanarwa.