Gwamnatin Jigawa Zata Hada Kai Da Saudiyya Domin Habbaka Harkokin Noma Da ilimi 



Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka a yayin da ya karɓi baƙuncin Babban Jakadan Ƙasar ta Saudi Arabia Yusuf Ibrahim Alghamadi a Gidan Gwamnati. 
Ya ce Jihar Jigawa ta ware fiye da kadada (eka) ɗari biyu domin noman alkama, a inda yayi kira ga Jakadan da ya miƙa buƙatar gwamnatin Jihar Jigawa ga gwamnatin Ƙasar ta Saudiyya don ganin yadda za a cimma nasarar samun haɗin gwiwar.
Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa harkokin ilimi shima wani ɓangare ne da gwamnatin jihar take so ta haɗa kai da ƙasar ta Saudiyya. 
A nasa jawabin, Babban Jakadan Ƙasar ta Saudi Arabia a Najeriya, Yusuf Ibrahim Alghamadi yace sun kawo ziyarar ne domin ƙarfafa danƙon zumuncin dake tsakanin Ƙasashen biyu (Najeriya da Saudiyya). 
Yace kasancewar a yanzu an kammala ayyukan faɗaɗa wuraren ibada na Masallatai biyu masu alfarma, gurbin da Najeriya ke da shi na Mahajjata, an ƙara a halin yanzu zuwa Mahajjata Dubu Casa’in da Biyar. 
Jakada Yusuf Ibrahim Algamadi yace ƙofofin ofishin jakadancin ƙasar Saudiyyan na Najeriya a buɗe yake ga duk masu neman aiki da su.

You may also like