Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Ayyana Dokar Ta Baci A Harkar  Kiwon Lafiya An ayyana dokar ta baci a harkar kiwon lafiya a jihar Bauchi. Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Barista Muhammad Abdullah Abubakar, 

ta dauki wannan mataki ne domin nuna rashin gamsuwar ta da kan yadda yanzu haka harkokin kiwon lafiya ke tafiya a jihar Bauchi duk kuwa da irin makudan kudin da Gwamnatin jihar Bauchi ke kashewa a harkokin kiwon lafiya a jihar.
Kwamishiniyar lafiya na jihar Bauchi Dakta Halima Muqaddas ce ta sanar da haka a Bauchi.
Haka kuma Kwamishinar ta sanar da sauke shugabannin gudanarwa na Babban Asibitin cikin su har da Babban Daraktan Asibitin kwararro na jihar Bauchi. Inda aka nada Babban sakatare na ma’aikatan lafiya Dakta Sa’idu Aliyu Getal.
Kwamishiniyar ta sanar da cewa Gwamnatin jihar ta amince da ware makudan kudade domin gyaran gidajen likitoci da ma gyara wasu  asibitoci a fadin jihar Bauchi.
Kwamishinan ta ce yanzu haka gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da  sauye-sauyen wuraren aiki ga ma’aikatan lafiya musamman ma wadanda suke birni a tura su kauyuka wuraren da aka fi bukatarsu, domin aiki ga jama’ar Bauchi.
Kwamishiniyar ta ce Gwamnatin jihar Bauchi ta dauki wadannan matakai ne domin inganta harkar kiwon lafiya a jihar da ma kawo karshen matsalolin kiwon lafiya a jihar.

You may also like