Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Fara Rabon Takin Zamani


Gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar,ya kaddamar da rabon takin zamani, ton 30,000 ga manoman jihar domin tunkarar noman damunar bana. 

Sanarwar da jami’in yada labaran gwamnan Abubakar Al-sadique, tace an kaddamar da rabon takin karamar hukumar Kirfi.

A cewar sanarwar gwamna Abubakar yayi farin cikin nasarar da aka samu a noman damunar shekarar da ta gabata da kuma na noman rani da manoman jihar suka samu. 

Takin mai yawan tan 30,000 za a siyar dashi ga manoman jihar a farashi mai rahusa na naira N5,000 akan kowanne buhun.

Gwamna Abubakar ya kara yawan takin daga ton 10,000 da aka siya aka raba a shekarar 2015 zuwa ton 30’000 da za a raba noman damunar shekarar 2017,wanda hakan zai taimakawa jihar dama gwamnatin tarayya a kokarin da ake na lalubo hanyoyin kudaden shiga da kuma rage dogaro akan man fetur. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like